Ba Abinda Buhari Ya Yiwa Najeriya Banda Jefata Cikin Halin Kunci Da Talauci – Sheikh Gumi


Shararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi ya ce zaben 2019 shi ne zabe mafi muni a tarihin Najeriya, kasancewar a lokacin ne aka zabi gwamnatin da bata tsinanawa jama’a komi karkashin jagoranci Muhammadu Buhari.
Sheikh Gumi ya furta wadannan kalaman nasa ne a lokacin da yake karbar bakuncin wani babban malamin addinin kirista, Isah El-Buba wanda ya ziyarcesa a gidansa dake Kaduna ranar Alhamis 
Gumi ya ce: “Zaben 2019 shi ne zaben da yafi ko wane zabe muni da takaici a tarihin Najeriya, saboda zabe ne wanda ya raba kan ‘yan Najeriya a bisa jahilci da rashin sanin ya kamata.
 “Bukatar mu ita ce mu samu shugaba wanda zai jagorance mu ba tare da nuna bambanci tsakanin wadansu bangarori ba, ina nufin wanda zai dauki dukkanin ‘yan Najeriya a matsayin diyansa.
 “Sai dai kuma kash akasin hakan ne abinda muke fuskanta a yanzu. Kawunan su rarrabu, ba kuma komi ya kawo wannan ba sai matsanancin talauci.

Duk miyagun laifukan da ake aikata a yanzu talauci ne ya kawo su. “Yan siyasa su ne masu kawo wa kasar nan matsala.
Wai gwamnatin dake ikirarin yaki da talauci kenan, sai ga shi an gano daya daga cikin gwamnoninta yana cusa daloli cikin aljihu. Babu abinda zai bamu cigaban da muke bukata a kasar nan idan ba sahihin zabe ba.” Inji Gumi.