Babbar Magana: Abinda DSS sukace kan batun sakin Zakzaky, Dasuki da Sowore

Zakzaky, Dasuki Da Sowore Ne Suka Roki Kotu Da Ta Taimaka Ta Barsu Da Zama A Hannun Mu Mai Makon Kurkuku –DSS

Hukumar tsaro ta sirri, DSS, ta bayyana babban dalilin da yasa take cigaba da rike tsohon mashawarcin shugaban kasa a kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki, shugaban yan Shia Ibrahim Zakzaky da kuma jagoran juyin juya hali na RevolutionNow, Omoyele Sowore.


Idan za’a tuna DSS ta ki sakin wadannan mutanen uku duk kuwa da cewa suna fuskantar shari’u a kotuna daban daban a Najeriya, sai dai hukumar tace mutanen sun gwammace su cigaba da zama a hannun DSS fiye da zaman gidan yari. 

Kaakakin hukumar DSS, Peter Afunanya ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a, inda yace Zakzaky, Dasuki da Sowore ne suka roki kotu da ta taimaka ta barsu su cigaba da zama a hannun DSS a maimakon a mikasu zuwa Kurkuku.