Babbar Magana: Ta Faru Ta Kare. An Bankado Wani Babban Sirri Akan Shariar Abba Gida Gida da Ganduje

PDP mai hamayya a Najeriya, ta ce akwai wani shiri a kasa da jam’iyyar APC da kuma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje su ke yi na canza Alkalan shari’ar karar zaben 2019.

Jam’iyyar adawar ta zargi APC mai mulki da gwamnatin Kano da yunkurin sauya Alkalan da za su saurari karar zaben gwamnan jihar da aka daukaka a gaban kotun daukaka kara da ke Garin Kaduna.

PDP ta bakin Sakataren ta na yada labarai, Kola Ologbondiyan, ta ce gwamnatin Abdullahi Ganduje ta na kokarin sauya Alkalan da aka zaba su saurari karar zaben jihar da wasu Alkalan na dabam.

Mista Kola Ologbondiyan ya ke cewa APC ta na son maye guraben Alkalan da kotun ta zaba ne da wasu Alkalan wadanda za su yi wa gwamnati mai-ci aiki a karar da Injiniya Abba Kabir Yusuf ya shigar.

PDP ta jawo hankalin jama’a ne a kan wannan shirin da ta ce ana yi a shari’ar da za a fara sauraro a makon nan.

An dage zaman farko ne daga Ranar 11 ga Nuwamba saboda an bada hutun aiki.

A cewar Mai magana da yawun bakin jam’iyyar ta PDP a Najeriya: “Tun kafi a soma zaman shari’a, Magoya bayan gwamna Ganduje sun fara murna su na cewa sun gama da kotun daukaka kara.”

“Jam’iyyar mu ta samu bayani mai inganci cewa dakatar da shari’ar da aka yi, shiri ne na canza Alkalan da aka riga a zaba da wasu da za su murde shari’ar domin jam’iyyar APC ta samu nasara.”

“‘Yan Najeriya su tuna cewa irin haka aka yi wajen zaben Alkalan kotun korafin zaben Kano, inda aka sauya Alkalan da za su saurari shari’ar, a karshe nasara ta tafi wajen Ganduje da kuma APC.”

“Jam’iyyar mu ta na kira ga shugabar kotun daukaka kara, Mai shari’a Zainab Bulkachuwa, da ka da ta bari a jefa ta cikin wannan tarka-tarka na taba teburin Alkalan da aka riga aka kafa.” Inji sa.