Babu maganar takun saka tsakanin Buhari da Osinbajo –Fadar Shugaban kasa

Babu maganar takun saka tsakanin Buhari da Osinbajo –Fadar Shugaban kasa


Fadar Shugaban kasa ta yi watsi da rahotannin cewa akwai wani rashin jituwa a tsakanin ofishin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da na mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Babban mai ba Shugaban kasa shawara na musamman akan harkokin majalisar dokokin tarayya, Sanata Babajide Omowurare ya bayyana hakan yayinda yake jawabi ga manema labarai a majalisar dokokin tarayya.

Da yake martani ga masu sukar lamari wadanda suka dasa ayar tambaya akan hukuncin shugaba Buhari na sanya hannu a wata doka a Landan, Sanata Omowrare ya ce lallai kundin tsarin mulki ta ba Shugaban kasar damar aiki daga ko ina.

Ya yi bayanin cewa lamarin ya sha banban da na tsohon Shugaban kasa Umaru YarAdua da mataimakin Shugaban kasa Goodluckk Jonathan inda ta kai ;lokacin da tsohon Shugaban kasar baya iya aiwatar da ayyukansa saboda tsananin rashin lafiya.

Sai dai kuma ya yi gum da bakinsa kan dalilin da yasa Shugaban kasar bai aika wata wasika zuwa ga majalisar dokokin kasar ba, inda zai mika ragamar aiki zuwa ga mataimakin Shugaban kasa.