Bikin Kiristimeti: Za’a Karya Farashin Shinkafa, Duk Da Rufe Iyakoki

Rufe iyakokin Najeriya: Shinkafar Ogoja na gab da shiga kasuwa kan farashi mai rahusa 


Kamfanin Santuscom Agro-Hub Investment Nigeria Limited ta ce za ta karyar da farashin shinkafarta na Ogoja 
A cewarta ta fara girbe gonarta mai fadin hekta 1,000 a Okpoma, karamar hukumar Ayala da ke jihar Cross River 


Kamfanin ta ce shinkafar Ogoja za ta kasance a kan N14,000 gabannin bikin Kirsimeti da na sabon shekara Kamfanin Santuscom Agro-Hub Investment Nigeria Limited, wacce ke sarrafa shinkafar Ogoja, ta ce za ta karyar da farashin shinkafar na cikin gida domin ta fara girbe gonarta mai fadin hekta 1,000 a Okpoma, karamar hukumar Ayala da ke jihar Cross River. 
Shugaba kuma babban jami’in kamfanin Santuscom, Cif Paul Santus, ya bayyana hakan yayinda ya ke zantawa da manema labarai a kan kokarin gonar na son daidaita shinkafar gida da ya yi tashin gwauron zabi sakamakon rufe iyakokin kasar da aka yi. 

Cif Santus ya ce shinkafar Ogoja za ta kasance a kan N14,000 gabannin bikin Kirsimeti da na sabon shekara.
Tun bayan da gwamnatin tarayya ta rufe iyakokin kasar, farashin shinkafar ya tashi inda ake siyar dashi tsakanin N18,000 da N20,000 a kasuwanni. A wani laarin kuma, mun ji cewa Gwamnatin tarayya a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamba, ta sanar da cewa za ta dauki ma’aikatan noma 75,000 domin karfafawa manoma gwiwa wajen samar da kayayyakin amfani.

Ta kuma kaddamar da kungiyar kifi na Najeriya tare da kudirin habbaka harkar kifi na gida biyo bayan rufe iyakokin Najeriya don hana shigo da kifi da sauransu. 
Karamin ministan noma da cigaban karkara, Mustapha Shehuri, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin diban ma’aikata 75,000 a Maiduguri, jihar Borno, a lokacin ziyarar gani da ido a gine-ginen ma’aikatar gona da cigaban karkara na gwamnatin tarayya a arewa masu gabas.