Daga Karshe Anyi Rabon Gadon Marigayi Rabilu Musa Dan Ibro

Daga Karshe Anyi Rabon Gadon Marigayi Rabilu Musa Dan Ibro

An raba gadon ne bayan da yayi shekaru biyar da kwanta dama sakamakon ciwon hanta da yayi ta fama da shi

Marigayin ya rasu ya bar mata uku da ‘ya’ya 20 a duniya

Kamar yadda tashar tsakar gida ta samo daga jaridar yanar gizo ta Najeriya arewa a ranar Alhamis 1 ga watan Agustan da ya gabata na wannan shekarar, anyi rabon gadon jarumi Rabilu Musa dan Ibro da ya kwanta dama shekaru biyar da suka gabata.

Marigayin dan wasan barkwancin ya bar tsabar kudi a asusun ajiyarsa na bankin Union har naira miliyan 30.

Marigayin ya bar motocin tirela biyu da bus guda biyu. Ya mallaki gida daya a Gwarinpa Abuja.

Ya mallaki gidajen siyar da man fetur 2, daya a Wudil, dayan kuma a titin Yola a Kaduna. Akwai kuma gidan da yake aikin gininsa ba a kammala ba.

Marigayin ya rasu ne a ranar 9 ga Disambar 2014.

Mutuwarsa na daya daga cikin manyan rashi da aka yi wanda ta girgiza masana’antar Kannywood bayan rasuwar marigayi Ahmad S. Nuhu wanda ya rasu yana tsaka da tashensa a masana’antar.

Rasuwar kuwa ta jefa mutane da dama cikin alhini da jimami.

Kafin marigayin ya kwanta dama, shine shugaban ‘yan fim din arewa da harkar camama.

An haifi marigayi dan Ibro ne a garin Dan Lasan dake karamar hukumar Warawa dake Kano. Ya rasa rasu ne sakamakon fama da ciwon hanta da yayi.

Ya rasu yana da shekaru 47 a duniya inda ya bar mata 3 da ‘ya’ya ashirin.

Allah ya jikan marigayin jarumin barkwancin ya kuma sa aljanna makomarsa.