Kalli Hotuna: Yarinya mai shekaru 8 da kaninta, sun kashe dan jinjiri Mai Kwana 7

Wata yarinya ‘yar shekara 8 dan uwanta mai shekaru 6 sun kashe ‘yar uwarsu mai mako daya


Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a cikin Ofunwegbe Community da ke karamar Hukumar Ovi na jihar Edo a ranar Talata.

Shaidu  sun bayar da rahoton cewa mahaifiyarsu ta sanar cewa ’ya’yanta sun kashe’ yar’uwarsu wadda makonta ɗaya a duniya.

Wakilan jama’ar gari sun fara tunanin cewa ko wasa ne, kawai daga baya suka fahimci cewa hakika sun aikata laifin.

Da farko mutanen sun ji abin dariya ne kawai, amma sun firgita sun gano abin da ya faru gaskiya ne bayan an kama yaran biyu da duka.  Lokacin da aka yi tambaya sai suka shaida cewa sun kashe wannan jariri

An bayar da rahoton cewa an mika yaran ga Policean sanda don ƙarin bincike.