Kannywood: Abinda Maryam Yahaya Ta Komayi Bayan Sana’ar Film

Kannywood: Maryam Yahaya ta karkata daga harkar Fim zuwa sabuwar sana’a


Shahararriyar tauraruwar fina finan Kannywood, Maryam Yahaya ta fadada hanyoyin samun kudinta, inda ta karkata daga harkar fitowa a fina finai kadai don samun kudi zuwa wata sabuwar sana’a ta daban.


Maryam ta bude wani katafaren shagon yi ma mata kwalliya da wankin gashi ne a cikin birnin Kano, wanda ta sanya masa sunanta, kamar yadda ta bayyana a shafinta na kafar sadarwar zamani na Instagram @real_maryamyahaya.


An hangi yan uwa da abokan arzikin Maryam a wajen bikin kaddamar da katafaren shagon, fitattu daga cikin wadanda aka hanga a wajen har da jarumi Sarki Ali Nuhu.