KANNYWOOD: Ba zan taba yiwa matata kishiya ba – Ali Nuhu

KANNYWOOD: Ba zan taba yiwa matata kishiya ba – Ali Nuhu
Shararren jarumin Kannywood, Ali Nuhu ya bayyana cewa mata guda daya tal ya ke da burin mallaka a rayuwarsa kuma ita ce matarsa Maimuatu – Har ila yau Ali ya ce yara hudu ya ke burin haifa, sai dai ya ce mai sa tanadin da Allah ya yi masa ba
Ali ya ce bai da yan mata a masana’antar sai dai ‘ya’ya, sanan cewa ya fi kusa da darakta Hafiz Bello fiye da kowa a dandalin Fitaccen jarumin nan na Kannywood wanda ake yiwa lakabi da sarki mai sangaya, Ali Nuhu ya bayyana cewa mata guda daya tal ya ke da burin mallaka a rayuwarsa.
 A hira da ya yi da shafin BBC Hausa, jarumin ya jaddada cewa daga Maimuna babu kari domin ita daya ta ishe shi zaman gidan duniya.
Kan yawan yayan da yake burin mallaka a rayuwarsa, Ali ya ce yara hudu kacal yake son ya Haifa, amma kuma Allah ne ya baiwa kansa sani.
Da aka tambayi jarumin game da yawa yan matasan na Kannywood, Ali ya bayyana cewa bashi da yan mata sai dai ‘ya’ya, inda ya bayyana sunayen yaran nasa a matsayin Hadiza Gabon, Maryam Yahaya da sauran su.
kan shawarar da aka fi bashi a rayuwa; Ali ya bayyana cewa a fi bashi shawara ne kan abunda ya shafi harkokin sana’arsa, da kuma dangantakarsa da mutane har ila yau jarumin ya bayyana Hafiz Bello a matsayin a hannun damarsa a masana’antar duk da cewar ba kasafai ake ganinsu tare ba.
Ya ce hakan yyaamo asali ne tun zamanin yarantarsu domin a cewarsa tare suka taso har girmansu.
Ya kuma bayyana cewa darakta Hafiz shine mutumin da basu taba samun tangarda da shi ba a Kannywood.
Baya ga harkar fim, jarumin ya bayyana cewa yana harkar ado da kwaliyya wato fashion design da kuma kiwon kaji.
Game da inda ya ke uin ganin kansa nan da shekaru 10 masu zuwa, Ali ya ce a lokacin yana fata yin ritaya sannan ya ga kansa cikin yaransa, watakil ma harda jika.