Ministan Sadarwa Sheikh Pantami Ya Dakatar Da Biyan Kudade A Ofisoshin Jakadanci

Ministan Sadarwa Sheikh Pantami Ya Dakatar Da Biyan Kudade A Ofisoshin Jakadanci


Gwamnatin Nijeriya ta ba da umarnin dakatar da biyan duk wasu kudade cikin gaggawa a duk ma’aikatun gidan waya na Najeriya, NIPOST.

Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Pantami ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai magana da yawun sa, Uwa Suleiman, ranar Alhamis.

Sanarwar ta nakalto ministan yana cewa wasu mambobin ma’aikatan NIPOST na cin gajiyar amfani da tsarin biyan kudi na ma’aikatar don aikata wasu munanan ayyuka.

Ya umarci jama’a da duk abokan cinikin NIPOST su nace kan Point of Sales, PoS, ko ma’amala na banki, lokacin gudanar da kasuwanci tare da NIPOST.

Sheik Pantami ya kuma umarci Post Master General, PMG, da ya tabbatar da aiwatar da dabarun da za su kawo karshen jinkirin da ba a bukata wajen bayar da sabis ga abokan ciniki.

A cewar ministan, umarnin wani matakin ne na wucin gadi don magance cin hanci da rashawa a cikin tsarin.

“Babban halin da ake ciki na yanzu na jinkirtawa a ma’aikatun gidan waya ba zai dauke ta a ofishin Ministan wanda a ciki wanda ke lura da ayyukan NIPOST din ba.
“A halin yanzu muna aiki kan sarrafa injina ta yadda ya zama tsani na dindindin ga kalubalen.

“Daga nan na umarci Babban Sakatare Janar, cikin hanzari, dakatar da duk wasu tsare-tsaren biyan kudi da ake da su a cikin cibiyoyin da ke kasar nan.

Sanarwar ta ce: “Babban maigidan na Post ya tabbatar da cewa dukkanin ofisoshinsa sun koma ga Point of Sales, PoS, da ma’amala na banki nan da nan, ” in ji sanarwar.