Tirkashi: Za’a siyar da safar marigayi Micheal Jackson akan zunzurutun kudi $2m
|Safar Michael Jackson da aka sa a kasuwa domin sayarwa; Farashin zai fara daga $ 1-2 Million
Safar wadda Masha hurin mawakin yayi salon tafiyar wata da ita, za’a siyar da ita ne akan makudan kudade.
A cewar TMZ, akwai wata wasika daga matar Micheal Jackson da ke tabbatar da cewa Michael ya sa safar ne don wasansa na farko a yayin wani shirin TV na musamman.