Wata Sabuwa: Abinda Ya Faru Bayan Rikicin Gabon Da Amina Minal Kan Zargin Madigo


Babbar kotun tarayya mai lamba 2 dake Kano karkashin mai shari’a O.A Oguata, ta kori karar da jarumar fina-finan hausa  Amina Amal ta shigar kan fitacciyar jaruman nan Hadiza Gabon.

Tunda farko dai Amina Amal ta shigar da kara a kotun tana zargin cewa Hadiza Gabon ta ci zarafinta, tare da bata mata suna, inda ta nemi da ta biyata diyyar zunzurutin kudi har Naira miliyan hamsin.

Zaman kotun da ya gudana a ranar larabar nan 6 ga watan Nuwamban da muke ciki, mai shari’a O.A Oguata, ya kori karar sakamakon rashin gamsar da kotun da gamsassun hujjoji kan zargin daga masu kara.

Har ila yau lauyan mai kara Barista Abdulhalim Adamu ya bayyana cewa sun karbi wannan hukunci da kotu tayi, amma zasu daukaka kara zuwa gaba.