Yadda Zaka Sami 4gb Akan N500, MTN Sun Kawo Sabon Tsari

Kamfanin MTN wanda shine jagaba ta fuskar sadarwa a Najeriya kuma wanda yake da mafiya yawon masu amfani (customers/users).

A kokarin sa na gamsar da masu amfani da layin MTN, kamfanin ya sake bijiro da wani sabon tsari wanda ze bawa masu anfani da MTN damar samun data 4gb akan Naira 500.

Dakata! Kada kai saurin kiran *131*1# don duba wannan tsarin, abin ba haka yake ba, yanzu zan nuna hanya mafi sauki da zaka samu Kyautar 4gb akan Naira 500.

Ga matakan da za ka/ki bi wajen samun wannan data mai arha:

Yadda zaka samu garabasar samun 4GB Data a MTN

 1. Sayi sabon layin MTN, kayi masa rijista sannan kai activating.

 2. Chanza tsarin da layin yazo dashi zuwa MTN Yafun Yafun (Yawanci ma sabon layin MTN dashi yake zuwa), idan yazo dashi base ka chanza ba

 3. Kira * 131 * 1 * 1 # sannan ka danna 5 don amsa abinda suka rubuto maka, zasu baka 2GB akan N500.

 4. Sannan zasu ninka maka daga 2gb yakoma 4gb.

 5. Duk sanda Kai haka, zasu ninka maka daga 2gb zuwa 4g har tsawon wata hudu (4).

6. Data zatai expire bayan kwana biyu (2).


Muna farinciki da jin ra’ayinka, rubuta a kasa, mungode