Yan Nijeriya Miliyan 90 Ke Fama Da Mahaukacin Talauci – Minista Sadiya

Yan Nijeriya Miliyan 90 Ke Fama Da Mahaukacin Talauci – Minista Sadiya

Akalla ‘yan Nijeriya  miliyan 90 ke fama da mahaukacin Talauci in ji Ministar Ma’aikatar Ayyukan Agaji da kula da ibtila’i, Hajiya Sadiya Umar Faruk, inda ta ce wannan dalilin ne ma ya sanya gwamnati ta yanke shawarar fitar da su daga cikin wannan hali da suke ciki.

Majiyarmu ta labarto cewa; Sadiya na bayyana hakan a yayin da take gabatar da kasafin kudin ma’aikatarta na shekarar 2020 a ranar Litinin wanda ya kai naira biliyan 44.21 domin neman sahhalewar majalisar dokokin kasar nan.

Sadiya dai ta gurfana gaban kwamitin majalisar wakilai dake kula da ‘yan gudun hijira ne a karkashin jagorancin Mohammed Jega, inda ta bayyana musu cewa daga cikin ayyukan ma’aikatarta akwai magance abubuwan dake janyo ibtila’i, takaita hakan da kuma kulawa da wadanda abin ya shafa.

Ministar ta jaddada cewa ma’aikatarta za ta inganta tare da karfafa ayyukan jinkai da kuma na bada agaji a tsakanin masu ruwa da tsaki. Kasafin kudin ma’aikatar bada agajin ya kunshi N464,306,285 na kula da ma’aikata, miliyan N165 don sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar Borno da Bakassi. Naira miliyan 15 don shigar da yan gudun hijira 1000 tsarin inshoran lafiya, NHIS, N60m kudin mayar da ‘yan gudun hijira makaranta, N105m don samar da famfunan ruwa, N184m don sayen filayen da za a tsugunar da ‘yan gudun hijira a Abuja da Nasarawa, N100m kudin tallafi ga mutanen da suka koma garuruwansu a Arewa maso gabas da dai sauransu.

A nasa jawabin, shugaban kwamitin, ya bayyana farin cikinsa da kasafin, inda ya ce yana sa ran zai amfani ‘yan Najeriya matuka. Haka nan ya jinjina ma shugaba Buhari da ya kirkiri wannan ma’aikata domin ta kula da matsalolin ‘yan gudun hijira da ake fama dasu a Nijeriya.